A karo na uku yan takarar shugaban kasa a nan Iran sun gudanar da muhawar na ukku kan al-amuran da suka shafi al-adu da zamantakewa a jiya jumma’a, inda ko wanne daga cikinsu ya bayyana ra’ayinsa da kuma shirinsa kan abinda yashafi matsayin mata a kasar da kuma yadda zasu kyautata matsayin mata a kasar.
Kashi fiye da 90 % na mata a kasar Iran dai suna iya rubutu da karatu, sannan da dama daga cikinsu suna digiri na uku wato (PHd)
Duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun yi kokarin daga darajar mata amma har yanzun ana ganin akwai saura idan an dubi halin damata suke a kasar.
Yan takarar shugaban kasa wanda za’a zaba daya daga cikinsu, sun hada da Moustafa Pourmohammadi, Mohamad Bagher Ghalibaf, Masoud Pezeshkian, Amir Hossein Ghazizadeh, Saeed Jalili da kuma Alireza Zakani, kuma ko wannensu yabayyana matsayin sa dangane da wannan .
Har’ila yau ana saran za’a gudanar da wasu Karin mahawar tsakanin yan takarar, akan wasu maudu’an guda biyu.
A ranar 28 ga watan Yunin da muke ciki ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Iran karo na 14. Kuma hakan yafaru ne, bayan rasuwar marigayi shugaban kasa shahid Ibrahim ra’isi a ranar 19 gawatan Mayun shekarar da muke ciki. Bisa kundin tsarin JMI dai idan an rasa shuigaban kasa, ko saboda ya rasu ko kuma don ya sauka ko an sauke shi daga mukaminsa to dole ne a gudanar da sabon zabe a cikin kwanaki 50 daga ranar da babu kuwa a kan kujerar shugaban kasa