Limamin Tehran Ya Bayyana Hanyar Shugabanci Na Gari Ga Al’umma A Wasikar Imam Ali {A.S}

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Mutunta dan Adam da bunkasa ci gaban kasa su ne manufar gudanar da

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Mutunta dan Adam da bunkasa ci gaban kasa su ne manufar gudanar da shugabanci na gari daidai da koyarwar Alkur’ani

A hudubar sallar Juma’arsa ta yau a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hujjatul -Islam wal-Muslimin Mohammad Hassan Abu Tarab -fard, ya bayyana wasikar Imam Ali dan Abi-Talib (AS) ga Malik Ashtar a matsayin wata kwakkwarar shaida da take tabbatar da shugabanci na gari a kan tubalin Alkur’ani mai girma mai dauke da abin lura da cewa: A mahangar Musulunci, samar da tushen ci gaba da daukaka da kuma amsa bukatun dan’adam da ci gaban bil’adama ta hakika an bayyana su a matsayin manufofin kafa gwamnatin Musulunci.

Abu Tarabi Fard ya kara da bayyana cewa: Daya daga cikin mafi sarkakekkiyar hanya ta ilimin siyasa ita ce gwamnati da rukunnanta, yana tambaya kan yadda za a kafa gwamnati, halaye da dabi’unta, ‘yan siyasa da masu mulki, da kuma kulla alaka tsakanin masu mulki da al’umma, alakar da ke tsakanin jama’ar kasa da masu mulki, da yadda ake samar da cibiyoyin zamantakewa, siyasa, shari’a, tattalin arziki, gudanarwa da dukkan bangarori da kusurwoyin ka’idar kasa a cikin tunanin siyasar Musulunci, duk wadannan sun zo cikin wasikar Imam Ali (AS) ga Malik Ashtar. Da yake bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin kyakkyawar dabi’a da mulki, yana mai jhaddada cewa: Idan jami’ai da ‘yan siyasa suka maida hankali kan wannan wasika, za mu fuskanci gagarumin sauyi ta kowane bangaren na tafiyar da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments