Yahudawan Sahayoniyya Sun Dawo Daga Rakiyar Netanyahu Tare Da Fifita Benny Gantz

Kuri’ar jin ra’ayin yahudawan sahayoniyya yana nuni da cewa: Benny Gantz ya fi fira ministan yahudawan sahayoniyya Benjamin Netanyahu farin jini Wani kuri’ar jin ra’ayin

Kuri’ar jin ra’ayin yahudawan sahayoniyya yana nuni da cewa: Benny Gantz ya fi fira ministan yahudawan sahayoniyya Benjamin Netanyahu farin jini

Wani kuri’ar jin ra’ayin jama’ar da akagudanar a haramtacciyar kasar Isra’ila da aka buga sakamakonsa a yau Juma’a ya nuna cewa: Shugaban jam’iyyar adawa ta “National Camp”, Benny Gantz ya fi fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu farin jinni, kuma da za a gudanar da zabe a halin yanzu shi ne zai lashe zaben fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, ba Benjamin Netanyahu ba.

A cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu “Wafa” ya watsa rahoton cewa: Kashi 42% na yahudawan sahayoniyya da suke zaune a yankunan Falasdinawa da aka mamaye sun bayyana a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta buga, za su gwammace Gantz ya zama fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila a kan Benjamin Netanyahu da za a gudanar da zabe a halin yanzu, yayin da kashi 35% suke ci gaba da goyon bayan Netanyahu, kuma wasu kashi 23% suka ce ba su da takamaiman ra’ayi.

Kuri’ar ta nuna cewa: Idan aka gudanar da zabe a halin yanzu, “Jam’iyyar National Camp” ce za ta samu nasarar lashe kujeru 23 (idan aka kwatanta da 12 da take da shi a halin yanzu) daga cikin kujeru 120 na majalisar dokokin kasar Knesset, yayin da jam’iyyar Likud da take karkashin jagorancin Netanyahu za ta samu kujeru 22 (idan aka kwatanta da kujeru 32 da take da su a halin yanzu.

Jam’iyyar “There is a Future” karkashin jagorancin madugun ‘yan adawa Ya’ir Lapid za ta samu kujeru 16, yayin da jam’iyyar adawa ta dama ta “Isra’ila gidan mu” karkashin jagorancin Avigdor Lieberman, za ta samu kujeru 14.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments