Isra’ila : ‘Yan Sanda Sun Murkushe Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnatin Netanyahu

‘Yan sanda a Isra’ila, sun tarwatsa zaman dirshin da zanga-zangar kin jinin gwamnatin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Kafofin yada labarai a kasar da dama sun

‘Yan sanda a Isra’ila, sun tarwatsa zaman dirshin da zanga-zangar kin jinin gwamnatin firaministan kasar Benjamin Netanyahu.

Kafofin yada labarai a kasar da dama sun wallafa hotunan yadda ‘yan sandan ke amfani da karfi wajen tarwatsa masu zaman dirshin a shigar birnin Kudus.

Haka kuma an kama da dama da suka tsohe wata hanya a birnin na kUdus.

Tunda farko dama dubban ‘yan kasar  sun taru a kan tituna kusa da majalisar dokokin kasar a birnin Kudus domin nuna adawa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu tare da neman a gudanar da zaben wuri tare da musanya fursunoni da kungiyar Hamas.

Masu zanga-zangar sun cika titunan, dauke da tutocin Isra’ila da kuma hotunan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken “A kawo karshen gwamnati mai yaudara,” “Zabe a yanzu,” “Maciya amana” da “Kunya,” kamar yadda kafafen yada labaran Isra’ila da dama suka nuno kai tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments