‘Yan Houthi Sun Yi Tir Da Amurka Kan Ayyana Ayyukansu A Teku Da Na Ta’addanci

Kungiyar gwagwarmayar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthis a kasar Yemen ta yi Allah-wadai da Amurka kan ayyana ayyukan da suke na

Kungiyar gwagwarmayar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthis a kasar Yemen ta yi Allah-wadai da Amurka kan ayyana ayyukan da suke na goyan bayan Falasdinu ta hanyar yaki da Isra’ila a matsayin  ta’addanci.

Kungiyar ta bayyana matakin na Amurka da wani yunkuri na boye halin da Falasdinawa ke ciki a zirin Gaza sakamakoin ta’addancin da gwamnatin Isra’ila ke aiwatarwa a Gaza.

“Ayyukan soji na Yemen gaba daya suna bisa ka’ida, kuma suna da nufin kare hakin dan Adam, za kuma su daina da zarar hare-haren wuce gona da iri da ake ci gaba da yi a Gaza sun daina,” a cewar ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bukatun kungiyar Ansarallah a bayyane suke: Za mu dakatar da ayyukan soji da zarar an kawo karshen farmakin da ake kai wa Gaza, tare da dage killacewar da aka yi wa mazauna yankin.

Sanarwar ta kuma ce : Kungiyar na yaba wa zanga-zangar goyan bayan Falasdinu da ke ci gaba da yaduwa a jami’o’i a fadin Amurka da kasashen yammacin duniya, wadanda ke neman kawo karshen kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza,” in ji Ansarullah.

Hare-haren na Ansarullah dai sun tilastawa wasu manyan kamfanonin jigilar kayayyaki da mai na duniya dakatar da zirga-zirga ta daya daga cikin muhimman hanyoyin kasuwancin teku a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments