Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya gabatar da tambayar cewa: Su wane ne wadanda suke ba da kariya ga yahudawan sahayoniyya suke aikata munanan laifukan ta’addancin ci gaba da kashe kananan yara da fararen hulan Falasdinawa a kullum rana?! Kan’ani ya jaddada cewa: Wadannan mayaudara masu karyar kare hakkin bil’adama marasa kunya ne suke kare yahudawan sahayoniyya da dukkanin karfinsu.
Wannan ya zo ne a cikin wani rubutu na yanar gizo da Nasir Kan’ani ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a jiya Litinin. inda ya kara da cewa: Kakakin Asusun Kare Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa: Yakin Gaza yaki ne kan kananan yara.
Kakakin Asusun na “UNICEF” ya kuma yi nuni da cewa: Yakin da ake yi a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane mafi yawa a tsakanin abokan aikinsa, idan aka kwatanta da sauran tashe-tashen hankula a tsawon tarihin wannan Hukuma ta kasa da kasa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ci gaba da cewa: A nan wannan tambaya ta taso ne: saboda duk wadannan abubuwa masu raɗaɗi da ban tsoro, sune suke bai wa yahudawan sahayoniyya da shugabanninsu damar aiwatar da laifukan kashe-kashen gilla kan yara tare da izinin ci gaba da kisan kiyashin da suke yi a kullum rana kan al’ummar Falasdinu, a kan idon duniya, kuma kungiyoyin kasa da kasa da na kare hakkin bil’adama suna gani babu wani mataki da suka na kalubalantar wannan ire-iren zaluncin. Yana mai jaddada cewa wadannan mayaudara ne suke da’awar kare hakkin dan adam.