Isra’ila ta ce an kashe mata sojoji takwas, a lokacin wani samame a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.
Rundunar sojin Isra’ilan ta ce dakarun suna tafiya ne a cikin motar sulke a lokacin da wani bom ya tashi da su.
To saidai kungiyar Hamas ta ce ta harba wata roka a kan motocin yakin Isra’ila, kuma sun yi ikirarin nasarar harin.
Rundunar ta kuma ce an kashe wasu sojoji biyu a arewacin Gaza a ranar ta Asabar a lokacin da wani bam ya tashi a kan tankarsu.
Wannan ya sanya adadin sojojin na Isra’ila da aka Kashe ranar Asabar, ya kasance mafi muni tun watan Janairu a yankin.
Adadin sojojin Isra’ila da aka kashe tun bayan mamayar Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba zuwa akalla 307, a alkalumman da shafin yanar gizon sojojin na Isra’ila ya fitar.
A wani labarin kuma Isra’ila ta sanar da abin da ta kira dakatar da aikin soji na kowacce rana a wasu yankunan arewacin Gaza.
A wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar, ta ce sojoji za su tsagaita ayyukansu tsakanin karfe 8 na kowacce safiya zuwa 7 na dare, a hanyoyin da suka dangana da Kerem Shalom zuwa titin Salah al-Din.