Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Bukaci Mutane Su Fito Don Zaben Shugaban Kasa A Zabe Mai Zuwa

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Aliyul Khaminaee ya bukaci mutanen kasar wadanda suka cancanci kada kuri’a su fito kwansu

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Aliyul Khaminaee ya bukaci mutanen kasar wadanda suka cancanci kada kuri’a su fito kwansu da kwarkwatansu don zaben shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabr a lokacinda yake ganawa da matasan da suka sami lambobin yabo a gasannin da suka shiga a cikin kasa da kuma kasashen waje.

Imam Khaminaee ya kara da cewa ‘wadanan matasa task ace ga kasar Iran, don haka su yi kokarin ganin sun nemi hanyoyin warware matsalolin da kasar take fama da su a duk inda suka sami kansu.

Ya kuma kara da cewa yakama su fadakarda iyalansu da abokansu das u fito don zaben shugabn kasa mai zuwa, kuma su zabi wanda yake mutunta al-amuran JMI da kuma ikidun da aka ginata a kansu.

Daga karshe jagoran ya bayyana cewa da alamun JMI tana da wani gagarumin rawar da zata taka a fagen kasa da jasa nan gaba don tabbatar da adalci da zaman lafiya a duniya. Don haka bukaci mutanen kasar musamman matasa su yi kokarin bada gudumawarsu don kaiwa ga wadannan manufofi masu muhimmanci ga dukkan duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments