Gwamnatin Kasar Sweden Ta Sake Hamid Nouri Wani Tsohon Jami’an Ma’aikatar Sharia Na JMI Da AKe Tsare Da Shi

Wani jami’in hukumar kare hakkin bil’adama a kasar Iran ya bada labarin sakin Hamid Nouri daga gidan yari a kasar Sweden Tashar talabijin ta Presstv

Wani jami’in hukumar kare hakkin bil’adama a kasar Iran ya bada labarin sakin Hamid Nouri daga gidan yari a kasar Sweden

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kazem Gharib Abadi shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta musulunci yana fadar haka a yau Asabar a shafinsa na X ko tweeter a da.

Hamid Nouri dai tsohon jami’in ma’aikatar sharia na JMK wanda ya shiga hannun jami’an tsaron kasar Sweden shekara ta 2019, tare da tuhumarsa da kashe yan adawar JMI wato MKO a lokacinda yake aiki a ma’aikatar shari’ar kasar.

Kazem Gharibabadi, yace an sami nasarar kubutar da Hamid Nouri daga gidan kaso a kasar Sweden ne tare da kokari na jami’an ma’aikatar sharia kasar Iran, ma’aikatar leken Asiri da kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar musamman marigayi shaheed Dr Hussain Amir Abdullahiyan .

Dan Hamid Nouri Majid Nouri ya aika da sakon sanar da jama’a kan cewa an saki mahaifinsa daga gidan kao a kasar Sweden, kuma a halin yanzu yana kan hanyarsa ta dawowa gida. Bayan kawanaki 1,680 a tsari a gidajen yarin kasar.

Majid yace zasu yi bukukuwan salla babba da kuma sallar Ghadir tare da mahaifinsu a nan Iran idan All..ya yarda.

Gwamnatin kasar Sweden ta kama Hamid nuori ne a lokacinda ya isa kasar Sweden a shekara 2019, tare da bukatar Iraniyawa mazauna kasar wadanda suke adawa da JMI. Iraniyawan suna zarginsa da hannu a kisan da aka yiwa yayan kungiyar MKO a kasar Iran bayan keshe kashen da suka aikata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments