Ana Kiraye-kirayen Yin Zanga-zanga Gabanin Jawabin Netanyahu A Majalisar Dokokin Amurka

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin yin wani jawabi a majalisar dokokin Amurka a watan Yuli, matakin da ke janyo kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga a

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin yin wani jawabi a majalisar dokokin Amurka a watan Yuli, matakin da ke janyo kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga a fadin Amurka.

Shugabannin majalisar sun sanar da ranar 24 ga watan Yuli a matsayin ranar da zai gabatar da jawabi.

A cikin wasikar da suka rubuta wa Netanyahu, Kakakin Majalisar Mike Johnson da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa Mitch McConnell – dukkansu ‘yan Republican – sun ce an mika goron gayyata ne don “karfafa dangantakarmu mai dorewa da kuma nuna hadin kan Amurka da Isra’ila.”

Saidai Gayyatar, ba ta samu amincewar jam’iyyar Democrat ba.

Gayyatar ta zo ne a daidai lokacin da alakar Tel Aviv da Washington ta yi tsami game da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Hare-haren da gwamnatin mamaya ta kai ya zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 36,654, akasarinsu. mata da yara, tare da jikkata wasu 83,309 a zirin Gaza.

A halin da ake ciki kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC na neman sammacin kama Netanyahu da wasu jami’an Isra’ila, bisa zargin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza da aka yi wa kawanya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments