Gaza: HKI Ta Kashe Yara Kanana Har Kimani 15,000 A Gaza A Cikin Watanni 8 Da Suka Gabata

Ma’aikatar Lafiya a yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kashe yara kanana zuwa gunduwa gunduwa har

Ma’aikatar Lafiya a yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kashe yara kanana zuwa gunduwa gunduwa har kimani 15,000 daga ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata zuwa yanzu.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar tana bada wannan rahoton a dai dai ranar yara ta duniya, wadanda aka cutar wato (the International Day of Innocent Child Victims of Aggression).

Rahoton ya kara da cewa banda wannan sojojin yahudawan sun kashe wasu Karin yara kanana 64 a yankin yamma da kogin Jordan a cikin wannan lokacin, daga cikin har da wadanda suka kashe a gabacin birnin Kudus.

Rahoton ya kara da cewa yaran gaza a bana sune suka fi ancanta da wannan suna a duk duniya. Sannan an hana daliban makaranta 620,000 zuwa makaranta a yayinda wasu 88,000 sun kasa zuwa jami’o’ii.

Wata kungiya mai zaman kanta ‘Euro-Mediterranean Human Rights Monitor’ wacce take aiki don kare hakkin bil’adama ta bada sanarwan cewa, sojojin HKI sun rusa makarantu kama  daga Jami’o’ii zuwa sakandari nasari da kuma na wasan yara. Banda haka ta kashe wasu yaran da dama a lokacinda suke barci.

Banda haka ta hana abincin yara da ruwa sha shigowa Gaza har ya kai ga wasu yara sun mutu saboda karancin abinci da kishin ruwa a Gaza.

A halin yanzu an kiyasta cewa yara kimani 3500 suna fuskantar barazanar mtuwa saboda rashin abincin yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments