Iran: Ministan Harkokin Waje Na Rikon Kwarya Zai Ziyarci Lebanon Da Siriya A Kokarin Kawo Karshen Yaki A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran na riko Ali Bakhiri Kani ya bayyana cewa marigayi shugaba Ra’isi da kuma ministansa na harkokin waje marigayi Dr Hussain

Ministan harkokin wajen kasar Iran na riko Ali Bakhiri Kani ya bayyana cewa marigayi shugaba Ra’isi da kuma ministansa na harkokin waje marigayi Dr Hussain Amir ABdullahiyan sun yi kokarin ganin an dakatar da bude wuta a Gaza, a cikin watanni 8 da suka gabata. Sanna a halin yanzu ma gwamnatin kasar tana kokarin shirya  taro na gaggawa na kasashen musulmi don tattauna wannan batun.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, Bakiri Kani zai ziyarci kasahsen Syriya da Lebanon a a cikin yan kwanaki masu zuwa don tattauna tare da jami’an gwamnatocin wadannan kasashe dangane da halin da ake ciki a Gaza da kuma yadda za’a tsagaita budewa juna wuta a yankin.

Kani ya kara da cewa a ranar Jumma’a sun tuntubi wasu kasashen musulmi don ganin yadda za’a kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza.

Daga karshe ya kammala da cewa yana saran za’a gudanar da taro dangane da hakan a daya daga cikin kasashen musulmi, ko kuma birnin Jidda na kasar Saudiya inda cibiyar kungiyar kasashen musulmi ta OIC take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments