China Ta Bayyana Cewa hakurinta Na Da Iyaka Dangane Da Takalar da Amurka Take Mata A Kudancin Tekun China

Ministan tsaron kasar Chaina Dong Jun wanda yake jawabi a taron tattaunawa ta ‘Shangre-La’ karo na 21 a birnin Singapore ya bayyana cewa hakurin kasar

Ministan tsaron kasar Chaina Dong Jun wanda yake jawabi a taron tattaunawa ta ‘Shangre-La’ karo na 21 a birnin Singapore ya bayyana cewa hakurin kasar Chaina yana da iyaka, musamman dangane da takalar da gwamnatin kasar Amurka tare da hadin kai da kasar Philippine suke yi a kudancin tekun Chaina.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Jun yana fadar haka a yau Lahadi a taron tattaunawa kan al-amuran tsaro a yankin.

Ministan ya kara da cewa shigo da makamai masu linzami samfurin ballistic wanda kasar Amurka ta yi zuwa kasar Philipine ya tada hankalin kasar China, kuma hakan yana iya kaiwa da ga kasa hakuri a kan abinda Amurka da kasar Philipine suke a kudancin tekun China.

Banda haka jun ya kara da cewa a wasu lokutan kasar Amurkan takan yi itisayen sojen ruwa tare da kasar Philipine a tekun kudancin chaina wanda hakan takala ne a fili ga kasar ta China.

Kasar Amurka ta hada kai da kasar Philipine don tunkarar abinda suka kira barazanar kasashen China a yankin Asia-Pecific.

Daga karshen yace Manila tana neman tashin hankali da kasar Chaina a dai dai lokacinda take atisayen soje da kasar Amurka a kusa da kasar China.

Daga karshe ministan yace gwamnatin kasar Chaina tana sanya ido a kan duk abinda yake faruwa a ruwan Tekun Kudancin Chaina. Kuma zata dauki matakan da suka dace a lokacinda ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments