Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a zirin Gaza bayan da babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da umarnin dakatar da kai farmaki
Isra’ila ta kai hare-hare a zirin Gaza ciki har da Rafah, duk da umarnin da babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na ta dakatar da farmakin da sojojinta ke kai wa kudancin birnin.
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hari a wasu sassan Rafah da kuma birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza a safiyar yau Asabar, kwana guda bayan da kotun kasa da kasa da ke birnin Hague ta umurci Isra’ila da ta gaggauta dakatar da kai hare-haren soji kan Rafah da yaki ya daidaita.
“Muna fatan matakin da kotun ta dauka zai sanya matsin lamba ga Isra’ila ta kawo karshen wannan yaki saboda babu wani abu da ya rage a nan,” in ji wata ‘yar Falasdinu wadda tayi gudun hijira daga birnin Gaza zuwa Deir al-Balah.
Harin da aka kai a yau Asabar, ya tabbatar da cewa Isra’ila ba ta wata alama ta shirin canja aniyarta Rafah ba.
“Isra’ila wata hukuma ce da ke daukar kanta a birbishin doka. Saboda haka, ban yi imani za ta kawo karshen da take yi a cikin sauki ba, inji Mohammed Saleh, wani mazaunin Gaza kamar yadda ya shaidawa manema labarai.
Isra’ila ta kai farmaki ta kasa a Rafah, inda dubban daruruwan Falasdinawa suka fake, duk da gargadin da kasashen duniya suka yi kan mummunar illar da hakan zai haifar ga ayyukan jin kai, wanda kuma hakan ya zuwa yanzu ya tilastawa sama da mutane 900,000 tserewa daga birnin.
A hukuncin da ta yanke a jiya Juma’a, babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, dole ne gwamnatin ‘yan mamaya ta dakatar da kai hare-haren soji, da kuma duk wani mataki da za a dauka a yankin Rafah, wanda zai iya jefa Falastinawa cikin hali na kunci.
A farkon makon nan ne Hukumar Ba da Agaji da Ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta ce kashi 75 cikin 100 na al’ummar Gaza, Isra’ila ta tilasta musu yin gudun hijira daga muhallansu.
Isra’ila ta kashe mutane fiye da 35,800, akasari mata da yara, tare da jikkata wasu fiye da 80,200 a Gaza, tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da ta kaddamar da mummunan yaki a Gaza, bayan da kungiyar gwagwarmayar Hamas ta kai farmakin ramuwar gayya a kan sojojin yahudawa ‘yan mamaya.