Iran : An Binne Gawar Shahid Amir-Abdollahian A Kudancin Tehran

An binne gawar ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian a kudancin birnin Tehran bayan shafe kwanaki ana gudanar da jana’izar wanda ya samu halartar

An binne gawar ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian a kudancin birnin Tehran bayan shafe kwanaki ana gudanar da jana’izar wanda ya samu halartar miliyoyin jama’a a garuruwa da dama.

Amir-Abdollahian ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar ranar Lahadi tare da shugaban kasar Ebrahim Raeisi da wsu jami’an kasar.

Dubun dubatar jama’a ne suka hallara a garin Shahr-rey da ke lardin Teheran yau Alhamis don gudanar da jana’izar, wanda aka kammala da binne shi a hubbaren Shah Abdolazim.

Ministan harkokin wajen kasar na riko, Ali Bagheri Kani, wanda ya halarci bikin, ya bayyana Amir-Abdollahian a matsayin shahidi wanda ya yi tsayin daka da riko bias tafarkin da kasar ke kansa a ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan’ani, wanda shi ma ya halarci jana’izar, ya ba da tabbacin cewa, “ba za a samu cikas ba a fannin manufofin ketare da huldar kasa da kasa ba”.

 “Ba shakka rashin Amir-Abdollahian rashi ne ga tsarin diflomasiyya na Iran, amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tsari ne da ya ginu a kan cibiyoyi da hanyoyin da suka dace a fagen alaka da manufofin ketare da suka taso daga tunani da manufofin Imam Khomeini.

Kan’ani ya jaddada cewa tsarin siyasar Iran yana da karfi da kuma iya aiki, inda ya ba da misali da yadda kasashe daban-daban a matsayi mafi girma suka halarci jana’izar marigayi shugaban kasar da mukarabansa.

Don haka, ko shakka babu ba za a samu wani cikas a kyakkyawar mu’amala da hadin gwiwar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen duniya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments