Shugabanni Da Wakilan Kasashen Duniya Da Dama Sun Halarci Jana’izar Shugaban Iran

Shugabannin kasashen duniya masu yawa da wakilansu sun halarci jana’izar shugaban kasar Iran da mukarrabansa tare da mika ta’aziyyarsu Shugabanin kasashen duniya da jagororin gwagwarmaya

Shugabannin kasashen duniya masu yawa da wakilansu sun halarci jana’izar shugaban kasar Iran da mukarrabansa tare da mika ta’aziyyarsu

Shugabanin kasashen duniya da jagororin gwagwarmaya da dama ne suka halarci taron juyayin jajantawa kan shahidan hatsarin jirgi mai saukar ungulu da ya ritsa da shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir Abdollahian da mukarrabansu.

Shugaban bangaren siyasar kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh ya halarci ta’aziyyar shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da sauran mukarrabansa a birnin Tehran. Kamar yadda kakakin kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Muhammad Abdul Salam ya halarci taron ta’aziyyar. Fira ministan Pakistan ya samu halartar ta’aziyyar. Haka nan Fira Ministan Iraki Muhammad Shiya’u Al-Sudani. Sannan mataimakin shugaban kasar Turkiyya kuma ministan harkokin wajen kasar. Wakili na musamman daga kasar Jordan. Wakili na musamman daga kasar Oman. Shugaban yankin Kurdistan na Iraqi. Shugaban Turkmenistan. Shugaban kasar Tunisiya. Fira ministan Siriya. Shugaban majalisar dokokin Lebanon. Sarkin kasar Qatar. Shugaban Rundunar dakarun sa-kai na Iraki. Mataimakin shugaban kasar China. Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah. Ministan Harkokin Wajen Belarus. Mataimakin shugaban kasar Indiya. Shugaban Majalisar Aljeriya. Bangarorin gwagwarmayar Falasdinu. Ministan harkokin wajen Kuwait Abdullah Al-Yahya. Ministan harkokin wajen Bahrain Abdullah Al-Yahya. Shugaban Majalisar Iraqi. Mataimaki na musamman ga Sarkin Saudiyya da Ministan Harkokin Wajen kasar ta Saudiyya. Ministan harkokin wajen UAE da sauransu.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments