Ministan harkokin wajen Norway, Espen Barth Eide, ya tabbatar da aniyar kasarsa na kame firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaro Yoav Gallant, idan suka shiga kasar bayan hukuncin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yanke a kansu.
Ministan harkokin wajen Norway, Espen Barth Eide, ya tabbatar a ranar jiya Talata cewa ya zama wajibi kasarsa ta kamo firaminista Benjamin Netanyahu idan ya shiga cikin kasar, domin aiwatar da hukuncin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yanke kan wannan batu.
A cikin wata sanarwa da wasu kafafen yada labarai na cikin gida suka bayar, ministan na Norway ya ce, “Idan akwai sammacin kama Netanyahu da Gallant daga kotun Hague, tabbas sai mun kama su idan suka shiga kasarmu.”
Bisa rahoton da gidan talabijin na Channel 2 na Norway ya bayar, ministan ya kara da cewa: “Yin hakan Dole ne a kan dukkan kasashen da suka sanya hannu kan amincewa da kotun ta ICC,” ya kara da cewa lamarin “ya shafi dukkan kasashen Turai.”
Eide ya jaddada cewa Norway ba za ta yi adawa da hukuncin kotun ICC ba, kuma a matsayinta na mamba a kotun ta ICC, tana goyon bayan aikin wannan kotu.
Ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa mai zaman kanta ce, kuma Oslo tana mu’amala da ita kamar sauran kotuna masu zaman kansu, yana mai nuni da mahimmancin ikon hukunta laifukan cin zarafin bil’adama.
Wannan na zuwa ne bayan da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa, Paris na goyon bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Cibiyar sadarwar “Bloomberg” ta Amurka ta buga labarin marubuci Andreas Kluth, inda ya yi magana game da matakai biyu da Washington ke dauka game da shari’o’in Kotunan Laifuffuka na kasa da kasa, yana mai jaddada cewa bai kamata shugaban Amurka ya yi watsi da hukuncin da za a iya yankewa shugabannin “Isra’ila”ba, yana mai jaddada cewa Amurka tana bin salon siyasar munafunci da harshen damo a kan wannan batu.”
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana bukatar mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na bayar da sammacin kama jami’an Isra’ila a matsayin abin kunya.