A Guinea-Bissau ‘yan kasar za su jira har zuwa ranar 26 ga Nuwamba, 2028, don kada kuri’a a zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisu na gaba.
An tsara gudanar da zabukan biyu a ranar 6 ga Disamban nan, a hukumance, saidai a cewar wata doka da Shugaban kasar na rikon kwarya Janar Horta N’Tam, an dage zaben da shekaru biyu.
Shugaban kasa ya ambaci rashin isassun, kayan aiki, da na kudi da ake bukata don gudanar da zaben.
Ya kuma jaddada bukatar tabbatar da halalci, tabbatar da gaskiya, hada kai, da kuma sahihancin tsarin zabe.
A lokacin jawabinsa ga ‘yan kasa, wanda aka watsa a talabijin na kasa, Janar Horta N’Tam Ya jaddada gyare-gyaren da aka yi don sabunta cibiyoyi da karfafa aikin Gwamnati.
“Dole ne a cika sharuddan sake fasalin siyasa,” in ji shi, yana mai bayyana cewa an riga an tsara kuma an ayyana wani muhimmin tsari na dokoki.
An kuma yi wa Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar kwaskwarima.