Ra’isi: Jinin Yara 15,000 Wanda HKI Ta Kashe A Gaza Ne Zai Kawo Karshen Wannan Haramtacciyar Kasar

Shugaban kasar Iran sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa jinin yara falasdinawa 15,000 wanda sojojin HKI suka kasha a Gaza a cikin watanni kimani 8

Shugaban kasar Iran sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa jinin yara falasdinawa 15,000 wanda sojojin HKI suka kasha a Gaza a cikin watanni kimani 8 da suka gabata, shi ne zai kawo karshen samuwar haramtacciyar kasar nan bad a dadewa ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Talata a jawabin day a gabatar a taron majalisar Imam Ridha (a) karo na 5 wanda ke gudana a halin yanzu a birni Mashad na kasar Iran.

Shugaban ya ce: Ba ma da wani kokwanto kan cewa rayukan yara kimani 15,000 da dojojin HKI suka dauke a gaza, sai sun zama sanadiyyar wargajewar wannan kasar, sannan adalci ya tabbata a duniya.

Jininn wadannan yara zai zama masomin sauda tsarin da ke tafiya a yau a duniya, zuwa wani tsari mai kamanta adalci da kuma dawo da zaman lafiya a doron kasa.

Shugaban ya yabawa daliban jami’o’iin Amurka wadanda suka fito a fili suna goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza, suka kuma bukaci a kawo karshen yakin da gwamnatinsu take tallafawa.

Shugaban ya kammala da cewa, Tare da yakin da ke faruwa a Gaza, mutanen duniya sun fara fahiuntar cewa tsarin dake tafiyar da duniya a yau bat sari ne da gaskiya da adalci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments