Iran Ta Bukaci Taron Gaggawar Kwamitin Tsaron Kan Amurka

Mataimakin Jakadan kasar Iran a MDD ya bukaci taron kwamitin tsaro na gaggawa don tattauna batun barazanar Amurka na amfani da babban bom samfurin GBU-43/B

Mataimakin Jakadan kasar Iran a MDD ya bukaci taron kwamitin tsaro na gaggawa don tattauna batun barazanar Amurka na amfani da babban bom samfurin GBU-43/B a kan kasar, da kuma barazanar Amurka.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gholamhossain Darzi yana fadar haka a wasikar da ya aikawa babban sakataren MDD Antonio Gotteress da kuma shugaban kwamitin tsaro na Majalisar a wannan watan.

Darzi ya bukaci kwamitin tsaron ya yi allawadai da Amurka da kuma HKI a barazanar sake farwa kasar da wani yaki inda a ciki Amurka tace mai yuwa ta yi amfani da manya manyan boma bomai kamar GBU-43 wanda ake kira ‘Uwar Boma bomai.

A cikin wasikar Darzi ya nakalto wasu kafafen yada labaran kasar Amurka suna bada wannan labarin sun kuma kara da cewa a wannan karon ma HKI zata kasance tare da Ita, sannan shi kansa Trump ya yi maganar wannan shirin a kafafen talabijan na kasar ta Amurka.

Israel Katsz ministan yakin HKI ya bayyana cewa kasarsa tana shirin sake kaiwa Iran wasu hare haren, inda a ciki zasu ragargaza dukkan cibiyoyin makamashi da bada wutan lantarki na kasar.

Labarin ya kamma da cewa a yake yaken da suka gabata HKI kadai ta jefa boma-bomai har 35,000 a kan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted