Shugaban Kasar Iran Ya Jinjina wa Al’ummar Kasar Kan Juriyarsu Na Fuskantar Makiya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Hakuri da jajircewar al’ummar Iran sun yi galaba a kan makiya da suke kokarin kunna wutar tarzoma a kasar

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Hakuri da jajircewar al’ummar Iran sun yi galaba a kan makiya da suke kokarin kunna wutar tarzoma a kasar

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa: Dalilin kiyayya da kyamatar al’ummar Iran da makiya ke yi, sun samo asali ne sakamakon ire-iren gagaruman nasarori da ci gaba mai ban mamaki da al’ummar Iran suka samu, inda ya fayyace cewa: Makiya sun yi kokarin haddasa fitina a kasar Iran a lokacin hargitsin da suka kunna na baya-bayan nan a Iran, amma mutane saboda hakuri da juriyarsu suka yi watsi da makirce-makircen makiya. A jawabinsa a zaman taron da ya hada al’ummar Iran da jami’an kasar da kuma baki ‘yan kasashen waje, Shugaban kasar Iran Sayyid Ra’isi ya jaddada cewa: Annabin Rahama, fiyayyen halitta, Muhammadu dan Abdullahi{s.a.w} da ya fi kowa gayyato mutane zuwa ga adalci da yin amfani da hankali da kyawawan dabi’u amma ya yi fama da makirce-makircen makiya da suke kokarin durkusar da kiransa, baya ga yunkurin kashe shi. Yana mai bayyana cewa: A yau irin wannan makircin ne mabiya Manzon Allah {s.a.w}suke fuskanta da kokarin hana al’umma yin riko da darajar Annabi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments