Iran: Amurka Ta Aiwatar Da MOU Na Islamabad Don Kawo Karshen Yaki

Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bukaci Amurka ta dawo kan takardun fahintar juna ta Islamabad ta aiwatar da abubuwan da suke cikinta, sannan

Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bukaci Amurka ta dawo kan takardun fahintar juna ta Islamabad ta aiwatar da abubuwan da suke cikinta, sannan a warware sauran al-amura a teburin tattaunawa idan tana son zaman lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis a lokacinda yake ganawa da Sheikh Mohammad bin Abdurrahman Al-Thani ministan harkokin wajen kasar Qatar kuma firai ministan kasar a nan Tehran.

Shugaban ya kara da cewa, Amurka da HKI basa son zaman lafiya a yankin yammacin Asiya, kuma basa son zaman lafiya tsakanin kasashen Musulmi. Yace kafin yakin da Amurka ta HKI suka dorawa JMI, akwai shirin aiwatar da wasu al-amura na tattalin arziki da siyasa  tsakanin kasashe Iran da Qatar amma hakan bai yu ba saboda halin da ake ciki.

Dr Pezeshkiyan ya godewa kasar Qatar kan kokarin da ta yi na dawo da zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka, kuma tana godewa sarki Tamim, godiya ta musamman kan wannan kokarin.

Yace, an dorawa kasar Iran yaki, bada takali wani da shi ba, don haka dole ne ta kare kanta, sannan ci gaba da wannan yakin ya cutar da kasar kuma yana ci gaba da cutar da ita, amma bata da zabi in banda ci gaba da yaki har zuwa lokacinda dayan bangaren zai zabi kawo karshen yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted