Tashar talabijan ta ‘nbc news’ ta Amurka ta bada labarin cewa manya manyan Jami’an sojojin kasar sun bawa shugaba Trump shawara dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz, inda suka bayyana cewa zai dauki lokaci za’a kuma zubar da jinin Amurkawa mai yawa sannan babu tabbas na samun nasara.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto abc News’ na cewa a halin yanzu Iran ta maida hankalinta gaba daya kan mashigar ruwa ta Hurmuz fiye da shirinta na makamashin nukliya.
Sai dai JMI ta sha nanata cewa, bata da wani shiri na mallakan makaman nukliya, kuma baya cikin tsaron tsaron kasar. Don haka ta haramta kera shi da ajiye shi ko kuma amfani da shi.
Kafin haka dai Trump ya sha akwashin fara wani yaki a Iran wanda ba’a taba ganin irinsa bat un yakin duniya na biyu, kuma a halin yanzu sojojin ruwa na Amurka ne suke iko da mashigar ruwa ta Hurmuz.
Mutanen Amurka suna sukan shugaban kan rashin ikon kwace mashigar ruwa ta hurmuaz daga hannun Iran al-hali wannan mashigar a bude take kafin su fermata da