Ma’aikatar sharia a kasar Amurka ta aike da sammacin kira zuwa kotu ga wasu yan jaridu a kamfanin jaridar New York Times dangane da wasu rahotanni da suka shafi tsaron jirnin fadar shugaban kasa samfurin Boeing wanda kasar Qatar ta bawa shugaba Trump kyauta a wata ziyarar da ya kai kasar a shekarum bayan.
Jaridar New York times ta bada labarin cewa wani jami’an ma’aikatar sharia wanda ake kira Jay Clayton ne ya rarraba sammacin gay an jaridun a gidajensu, tare da bukatar su halarci gaban alakali a ranar laraba mai zuwa.
Labarin ya kara da cewa ana tuhuman yan jaridun da bada rahoto na sirri danga ne da jirgin fadar shugaban kasa wato ‘Airforce One’ sabo wanda kasar Qatar ta Bawa trump .
Kafafen yada labarai da dama sun yi allawadai da sammacin, suna kuma ganin neman takurawa kafafen yada labarai masu zaman kansu ne a kasar.