IRGC Ta Ce Ta Lalata Cibiyar Bada Umurni Da Kuma wurin Gyran Jiragen Yakin Amurka A Qatar

Kamfanin dillancin labaran yaki na Tasnim ya nakalto wani bayani wanda bangaren hulda da jama’a na rundunar ta IRGC na cewa: Majiyar dakarun kare juyin

Kamfanin dillancin labaran yaki na Tasnim ya nakalto wani bayani wanda bangaren hulda da jama’a na rundunar ta IRGC na cewa:

Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ta bada sanarwan cewa ta lalata wata cibiyar bada umurni da kuma gyran jiragen yakin Amurka dake kasar Qatar a hare haren safiyar yau Lahadi.

Da sunan All.. Qasimul Jabbarin’ Duk wanda ya tsokaneku, ku rama gwagwadon Tsokanar da yayi maku. A maida martani ga hare-haren makiya mai kashe yara Amurka a kan wasu sansanonin sojojin IRGC a bakin ruwan tekun Farisa, dakarun su kai hare hare kan cibiyar cibiyar gyaran jiragen yaki da wuraren ajiyarsu da kuma cibiyar gudanar da harkokin yakin na Amurka dake kasar Kuwait, wannan bayan sun lalata jirgin ruwan Amurka na biyu wanda yake kokarin wucewa ta mashigar ruwa ta Hurmuz ba tare da izinin Iran ba.

Makiya, Amurka da HKI su san cewa, idan sun ci gaba da keta hurumin Iran zasu ci gaba da gamuwa da makamai masu linzami masu nikawa na kasar Iran. Idan kun kawo hari zamu maida martani.

Sashen huldar Jama’a na IRGC.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted