A yau Laraba ne dai miliyoyin mutanen Iraki, su ka cika birnin Najaf mai tsarki domin yin bankwana da jagora shahidi Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a hubbaren Imam Ali (a.s).
Miliyoyin Irakawan ne sun fara taruwa ne a haramin Imam Ali ( a.s) tun da safiyar yau Laraba cikin nuna alhini.
Wakilin Ayatullah Sistani ne ya sallaci gawar jagora shahidi da kuma ta iyalansa da su ka yi shahada a tare da shi, kafin a zagaya cikin birnin na Najfa mai tsarki da su.
Daga Najaf an nufi birnin Karbala, a hubbaren Imam Hussain ( a.s) da kuma na Abul Fadal al-Abbas, domin yin bankwana da kuma samun tabarrukin iyalan gidan Manzon Allah masu tsarki.
A tsawon kan hanya miliyoyin mutanen Iraki da su ka fito daga mafi yawancin garuruwan kasar su ka yi wa gawar sahidin rakiya, cikin nuna bakin ciki da alhiji na babban rashin da al’ummar musulmi su ka yi.
Tun a jiya Talata da marece ne dai aka kai gawar jagora shahidin a filin saukar jiragen sama na birnin Najaf da ya sami tarbar Fira ministan kasar Ali Falih Kazim Zaidi, da kuma ‘yan siyasar kasar ta Iraki daga bangarori mabanbanta.
Daga nan Iran, shugaban kasa Mas’ud Pizishkiyan, da ministan harkokin wajen Dr.Abbas Arakci suna cikin wadanda su ka yi wa jagora shahidi rakiya zuwa Iraki.
A gobe Alhamis ne dai za a binne gawar jagora shahidin a hubbaren Imam Ridha ( a.s) dake birnin Mashhad a nan Iran.