Jama’a da dama a Iraki sun yi bankwana da gawar Imam Khamene’i da ya yi shahada a taron juyayin birnin Najaf
Birnin Najaf mai tsarki ya shaida isowar miliyoyin masu makoki na Iraki a ranar Laraba don halartar bikin bankwana da jana’izar Imam Sayyid Ali Khamenei, a cikin yanayi mai cike da baƙin ciki da juyayi, yayin da al’amuran suka nuna tarin jama’ar da suka cika kan titunan birnin don halartar bikin jana’izar.
Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa: Jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci da aka yi wa gawar shahidi Khamene’i ta nuna wa duniya irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin jama’a da gwamnati.
Bayan jana’izar jagoran juyin juya halin Musulunci da aka yi wa gawar shahidin a birnin Qum tare da daukarsa zuwa kasar Iraki, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: “An bayyana alaƙar da ke tsakanin mutane da gwamnati ga duniya a jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci da aka yi wa gawar shahidin.”