Ministan harkokin wajen Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya ce; Babban abinda yake kawo rashin zaman lafiya a cikin wannan yankin na yammacin Asiya da kuma yin barazana ga tsaronsa, shi ne laifukan yakin da HKI take tafkawa a cikin Gaza, da kuma yammacin kogin Jordan.
Hussain Amir Abdullahiyan wanda yake halartar taron kwamitin tsaro na MDD a birnin Newyork, domin tattauna batun tsagaita wutar yaki a Gaza, ya bayyana cewa; ya gana da takwarorinsa na kasashe, da su ka hada da na kasar Brazil Mauro Vieira inda su ka tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.
Da yake bayani akan harin mayar da martani da Iran ta yi akan HKI, Amir Abdullahiyan ya ce; harin yana a matsayin mayar da martani ne akan laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniya ta tafka, wanda hakan yana tafiya akan dokokin kasa da kasa.
Har ila yau ministan harkokin wajen ya yi gargadi akan duk wata tsokana da ‘yan sahayoniyar za su yi wa jamhuriyar musulunci ta Iran, domin za su fuskanci mayar da martani mai tsanani da ya fin a farko.
A nashi gefen, Mauro Vieira ministan harkokin wajen Brazil ya yi gargadi akan fadadar fagagen yaki a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, yana mai kara da cewa; Brazil tana son ganin zaman lafiya ya dawo a cikin yankin.