1
Bayan harin da aka kai wa Iran, Trump da jami’an Amurka sun sha nanata cewa suna son rusa tsohon tarihin Iran ko mayar da ita zuwa Zamanin Dutse, amma tambayar ita ce: wane tarihi ne muke magana a kai?
2
Tsohon tarihin Iran ba Magana c eta tarihi ba kawai; batu ne ne na al’umma da suka yi suna ta fuskar ilimi da kirkira da fahimta tun dubban shekaru da suka gabata.
3
Bari mu yi ɗan yi gajeren nazari kan wannan batu:
4
A cikin wani gari na Iran da aka ƙone, wato shekaru dubu biyar da suka gabata, ana iya ganin alamun tiyatar kwakwalwa, zane-zane na farko a duniya, da kuma abubuwa na ci gaba.
5
Kimanin shekaru dubu uku da suka gabata, Elam sun bai wa duniyar da ta daɗe sabon tsari wajen haɓaka rubutu, gine-gine, da tsarin gudanarwa ta hanyar kafa ɗaya daga cikin tsoffin ƙasashe masu tsari.
6
A Iran kafin Musulunci, Achaemenids, ƙarƙashin jagorancin Cyrus the Great a ƙarni na shida kafin haihuwar Annabi Isa, sun kafa hanyar habaka al’adu nakabilu da yawa; daga Indiya zuwa Bahar Rum.
7
Haka kuma, an rubuta “Cyrus Universal Charter” akan batun ‘yancin addini da kuma hana bauta.
8
A fannin addini tun a wancan lokacin, Zoroaster wanda shi ne ake bayyana shi da zulqarnain, ya dora su a kan kyakkyawan tunani, magana mai kyau, aiki mai kyau”, ya kafa ɗaya daga cikin tsarin ɗabi’a na farko a duniya.
9
Darius shi ma ya ƙirƙiri hanyar sadarwa ta duniya ta farko ta hanyar gina “Royal Road” wanda wani nau’in tsarin gidan waya ne a dad an adam ya fara amfani shi domin isar da sakonni.
10
Haka nan kuma bayan zuwan Musulunci, Iran ta zama cibiyar kimiyya. Al-Khwarizmi ya kafa hanyar lissafin aljebra.
11
Ibn Sina ya rubuta littafin Qanun kan magunguna, da kuma Al-shifa kan ilimin falsafa, wanda ya canja falsafar Girka.
12
Abu Raihan al-Biruni ya gabatar da wani sabon ilimin halayyar ɗan adam ga duniya ta hanyar nazarin yanayin mutanen Indiya, kuma Khayyam ya ƙirƙiri kalanda kwanan wata mafi daidaito a ƙarni na 11 da 12 bayan haihuwar annabi Isa.
13
A fannin al’adu, Ferdowsi ya haɗa tsarin maganganu masu ban mamaki da suke fayyace ɗabi’un ɗan adam a cikin littafinsa “Shahnameh” .
14
Mawaka kamar Saadi da Hafez sun yi magana game da halaye da ɗabi’u, Saadi yana cewa, ‘yan Adam asalinsu jiki ɗaya ne, wanda kuma an rubuta wannan jumlar tasa a cikin Majalisar Dinkin Duniya.
15
A zamanin Safawiyya, samar da ingantaccen tsaro a yankin Iran da Tekun Farisa sun taimaka wajen haɓaka kasuwancin duniya.
16
A yau, Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya fito da hakikanin fuskantar Amurka ta gaskiya da kuma Sahyuniyawa, kuma ya zama tushen gwagwarmaya da zalunci a duniya.
17
Al’umma mai tsohon tarihi da al’adu na dubban shekaru ne wasu ke barazanar za su rusa a yau, bayan hidima ga ilimi da ci gaban dan adam na tsawon dubban shekaru.