Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Oman Sun Tattauna Kan Zaman Birnin Geneva

Birnin Geneva ta karbi bakwancin taron tsakanin Araqchi da Al-Busaidi kafin a ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya

Birnin Geneva ta karbi bakwancin taron tsakanin Araqchi da Al-Busaidi kafin a ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Oman, Badr al-Busaidi, a Geneva domin tattauna shirye-shiryen karshe kafin a ci gaba da tattaunawa ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.

A yayin taron, Araqchi ya bayyana matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan dage takunkumi da kuma batun makamashn nukiliya.

An gudanar da taron ne bisa ga ka’idojin da aka tsara na tattaunawa da nufin daidaita kokarin kafin fara tattaunawa ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya nuna godiyarsa ga kokarin takwaransa na Oman na taimakawa ci gaban tsarin diflomasiyya da ake da shi, yana mai lura da cewa nasarar tattaunawar tana bukatar gaskiya daga daya bangaren da kuma gujewa daukar matsaya da halaye masu karo da juna.

A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Oman ya yaba da dagewar Iran wajen bin hanyar diflomasiyya don magance matsalar makamashin nukiliya, yana mai tabbatar da shirin kasarsa na ci gaba da kyawawan anufofinta da kuma samar da dukkan goyon baya don ci gaba da wannan tsari. Ya bayyana fatansa cewa wadannan shawarwari, tare da dagewa daga bangarorin da abin ya shafa, za su haifar da sakamako masu gamsarwa. A yau Alhamis ne aka shirya ci gaba da tattaunawar da ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, tare da halartar wakilai daga kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted