Babban Hafsan Sojojin Iran ya bayyana cewa: Sun shirya tsaf don faɗaɗa haɗin gwiwar soja da kasar Armeniya
Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Seyyed Abdolrahim Mousavi, ya tabbatar a ranar Talata, a lokacin ganawarsa da Ministan Tsaron Armeniya Soren Papikyan cewa: Shirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne fadada hadin gwiwar soja da Sojojin Armeniya.
Ya kara da cewa a yayin taron cewa: “Iran da Armeniya suna da dogon tarihi,” yana mai lura da cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin yana taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tsaro da kwanciyar hankali na yankin. Ya jaddada shirin Iran na bunkasa hadin gwiwar soja da Sojojin Armeniya.
Babban Hafsan Sojojin Iran ya kuma nuna cewa: Kasancewar kasashen waje a yankin ya saba wa muradun mutanenta kuma yana taimakawa ga rashin zaman lafiya a yankin. Ya bayyana cewa Amurka na kokarin tilasta ikonta ta hanyar haramtacciyar hanya, yayin da duniya ke fuskantar sauyi daga tsarin rayuwa daya zuwa tsarin rayuwa mai fadi da yalwa.
Manjo Janar Mousavi ya lura cewa “duk da hasarar da aka samu a yakin kwanaki 12 da aka kakaba wa Iran na kwanan nan da kuma shahadar kwamandoji, masana kimiyya, da ‘yan kasa, Sojojin Iran, tare da goyon bayan jama’a, sun sami damar tilasta wa abokan gaba su gabatar da shawarar tsagaita wuta.” Ya jaddada cewa Iran ba zata fara kaddamar da wani yaki ba, amma za ta mayar da martani da karfi ga duk wani kuskure da makiyanta suka yi.