Sabon Salon Mamayar Yankunan Falastinawa

Ka taba jin cewa idan aka jefa kwado a cikin tafasasshen ruwa, zai yi tsalle ya fita, amma idan aka yi ta dumama ruwa a

Share

Yankunan Falasdinawa suna cikin haɗari, rashin gida yana karuwa kowace shekara. Mamaya ba ta tsaya ba

Ka taba jin cewa idan aka jefa kwado  a cikin tafasasshen ruwa, zai yi tsalle ya fita, amma idan aka yi ta dumama ruwa a hankali a hankali, kwadon zai zauna a ciki har sai ya dahu.

A Yammacin Kogin Jordan, Isra’ila ba tare da sanarwar mamaya a hukumance ba, ta hanyar zartar da dokoki na gefe guda, ta canza rubutattun  ka’idoji.

Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da wasu tsare-tsare da suka sake fasalin tsarin  mamaya; matakin da mutane da yawa ke ganin cewa ya yi kama  da salon hadiyar maciji.

Bisa yarjejeniyar Oslo, yankin A yana karkashin cikakken ikon Falasdinawa, yankin B gwamnatin farar hula ta Falasdinu da jami’an tsaron Isra’ila, yankin C kuma wanda shi ne kusan kashi 60% na Yammacin Kogin Jordan, zai kasance karkashin cikakken ikon Isra’ila.

Amma yanzu ikon zartarwa na Isra’ila ya kai har  yankin A, bisa wasu dalilai kamar hana gine-gine marasa izini ko kare kayayyakin tarihi.