Mutane biyu wadanda aka fi sani dangane da kare hakkin Falasdinawa a kasar Burtania wato Ben Jamal na kungiyar ‘Palastine Solidarity campaign’ wato kungiyar masu goyon bayan falasdinawa da kuma Chris Nineham na kungiyar ‘Stop the war Coalations’ wato a kawo karshen kawancen yaki duk suna fuskantar sharia kan tuhumae sabawa dokar hana zanga-zanga ko gangami shekara guda da ta gabata.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yansanda a birnin Landan sun kafa dokar hana gangami a ranar 18 ga watan Jenerun inda wadanda suka shirya gangamin suke son ajiye furanni a kofar shiga BBC a birnin Landan don tunawa da yaran da aka kashe a kisan kiyashin Gaza.
Amma bayan da daruruwa ko dubban mutane suka sabawa wannan dokar daga cikin har da Nineham an kama kimani mutane dozen da dama, a halin yanzu an gabatar da su a gaban sharia tare da sabawa dokokin zamantakewa.
Masu goyon bayan Falasdinawa a kasar dai suna ganin hakan yan da nasaba da sabawa siyasar gwamnatin kasar Burtania, na goyon bayan yahudawan sahyonia da kuma hana masu goyon bayan Falasdinawa hakkinsu na fadin al-barkacin baki da kuma hakkinsu bayyana ra’ayinsu.
Wannan al-amarin dai ya bayyana cewa hakkin mutanen kasar Burtana na fadin al-barkacin baki sun fada cikin hatsari babba. Don idan an yi shiru zasu ci gaba da take hakkin mutane Kenan.