Kasar Habasha Ta Girke Dakaru A Tigray Saboda Fargabar Barkewar Yaki Tsakani

Gwamnatin Habasha ta sanar da girke dakaru akan iyakar yankin Tigray ta arewaci a wani yanayi da majiyoyin diflomasiyyar yammacin duniya ke ganin akwai yiwuwar

Gwamnatin Habasha ta sanar da girke dakaru akan iyakar yankin Tigray ta arewaci a wani yanayi da majiyoyin diflomasiyyar yammacin duniya ke ganin akwai yiwuwar barkewar sabon yaki tsakanin dakarun kasar ta gabashin Afrika da yan tawayen yankin.

Wasu majiyoyi sun ce sojojin na Habasha yanzu haka na kokarin yiwa yankin Tigray kawanya inda a baya-bayan nan mahukuntan kasar suka takaita yawan jiragen da ke ziraga-zirga a yankin, dai dai lokacin da majiyoyi ke cewa su kansu mayakan yan tawayen sun yi shirin tunkarar yaki da sojin na gwamnati.

Wannan na zuwa a dai dai lokacin da ake takun saka tsakanin Habasha da Eritrea bayan da Addis Ababa ta zargi Asmara da baiwa yan tawayen Tigray makamai, zargin da Eritrea take ci gaba da musantawa.

wani babban jami’in diflomasiyya da ke sanya ido kan rikicin na Tigray yace yanayin da ake ciki yanzu haka a yankin ba shi da kyau, domin yaki ka iya barkewa a kowanne lokaci wanda kuma ba a fatan faruwarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted