Dakarun kungiyar Hizullah ta kasar Lebanon sun yi luguden wuta a kan sansanin sojojio na Malikya a cikin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, sannan sun yi amfani da makamai daban daban wadanda suka hada da garkuwan tankunan yaki.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayani da kungiyar ta fitar a safiyar yau Asabar yana cewa, dakarun ha’ila yau sun yi luguden wuta kan gungun sojojin HKI a Ramiya da makaman atilary.
Kungiyar ta kara da cewa ta kai wadan nan hare hare ne don tallafawa Falasdinawa wadanda suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza. Kuma zata ci gaba da wadannan hare haren matukar an ci gaba da yaki a Gaza.
Tun kimani watanni 6 kenan kungiyar ta shiga yaki da sojojin HKI a arewacin kasar wanda ya kai ga halakar da dama daga cikinsu, da kuma jikatan wasu da dama.
Har’ila yau da kuma tilastawa dubban daruruwan yahudawan kauracewa gidajensu a yankin.