Wani Baban jami’in kasar Amurka ya sanar a jiya Talat ace, kasar tasa za ta aike da sojoji 200 zuwa Nigeria domin bayar da horo akan fada da kungiyoyin da suke dauke da makamai.
Dama a makon da ya shude ne dai sojojin Amurkan su ka sanar da cewa, sun aike da wata karamar tawagar soja zuwa Nigeria, da hakan ya zama furuci na farko da Amurkan ta yi akan cewa tana da sojoji a kasa a Nigeria.
A daren kirsimeti ranar 25 ga watan Disamba 2025 ne dai Amurka ta kai hari a Nigeria akan wuraren da ta ce, na masu dauke da makamai ne na kungiyar “Da’esh” ( ISIS).
Jami’in na Amurka ya ce, sojoji 200 da Amurkan za ta aike a yanzu, za su hade da karamar tawagar sojan da dama sun isa can Nigeria din domin taiamkawa sojojin kasar ta Nigeria.
Kamfanin dillancin Labarun Reuters ya ambato shugaban kasar Amurka Donald Trump yana cewa; Da akwai yiyuwar daukar wasu matakai na soja.”
Haka nan kuma kamfanin dillancin labarun na Reuters ya ce; Jiragen leken asirin Amurka suna yin shawagi a sararin samaniyar Nigeria,bayan sun taso daga sansanoninsu na kasar Ghana.
Donald Trump na kasar Amurka ya taba zargin Nigeria da cewa tana kashe Mabiya addinin kirista, lamarin da gwamnati da al’ummar kasar su ka karyata.
Da akwai kungiyoyi masu dauke da makamai a Nigeria da suke yi wa al’ummar kasar kisan mai kan uwa da wabi, ba tare da tantance addininsu ba. A lokuta mafi yawa, kungiyoyin sun fi yi wa musulmi kisan kiyashi, fiye da waninsu.
Tsawon shekaru 17 kenan kasar take fama da matsalar kungiyoyin dake dauke da makamai a arewa maso gabashinta da kuma arewa maso yamma.