Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ruwaito cewa akalla yara 37 ne suka mutu tun farkon shekarar nan ta 2026 a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.
Daraktan UNICEF a yankin na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Edouard Beigbeder, ya ce lamarin ya ci gaba da zama “mai matukar hatsari ga yara da yawa a Zirin Gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a watan Oktoban 2025.
A watan Janairu, mai magana da yawun UNICEF James Elder ya bayyana cewa an kashe yara sama da 100 na Falasdinawa, ciki har da yara maza 60 da ‘yan mata 40, a Gaza tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a watan Oktoban 2025.
” A halin yanzu, Elder ya nuna mummunan tasirin hare-haren Isra’ila kan sha’anin ilimi a Gaza, inda kusan kashi 90 cikin 100 na makarantu suka lalace, wanda ya bar yara sama da 700,000 ba tare da samun damar zuwa karatu akai-akai ba.
Isra’ila ta kaddamar da kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda ta kashe Falasdinawa sama da 72,027, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 171,651.