A yau Lahadi ce wadanda suka cancanci zabe a kasar Japan suke zaben yan majalisar dokoki kasar wadanda kuma zasu zabi firay minister nag aba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa gamayyar Jam’iyyu karkashin Firay minister mai ci Takaichi Sanae ne ake saran zasu lashe zaben.
Labarin ya kara da cewa Sanae Takaichi yar shekara 64 a duniya ta zama firay ministan kasar a cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce aka zabeta a kan kujerar Firay ministan kasar Japan, sannan ya zuwa yanzu ta sami karbuwa a kasar, don haka ana ganin tana iya samun nasara a zabe na yau wanda zai bada damar ci gaba da rike kujerar Firai minister.
Sanae Takaichi ta shahara a cikin yan watannin da suka gabata da shirinta na kara kashewa bangaren tsoron kasar Japan, kuma tana cewa idan kasar China ta kai hari kan Taiwan zata shiga yaki da Ita.
Masana suna ganin Jam’iyyarta ta Liberal Democratic Party (LDP) da ‘Japan Innovation Party, suna iya samun akalla kujeru 300 cikin 465 na majalisar dokokin kasar wanda zai bawa gamayyarsu damar kafa gwamnati.