Daruruwan lebirori ma’aikata a tashishin jiragen ruwa a wasu kasashen turai sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kwararar makamai daga kasashen zuwa HKI don kashe Falasdinawa.
Kafafen yana labarai na kasar Italia sun bayyana cewa daruruwan lebirori ma’aikata a tashar jiragen ruwa na Civita Vecchia mai tararar kilomita 60 daga birnin Roma babban birnin Italia sun gudanar da zanga- zangar nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnatocin kasashen turai suke son amfani da su don jigilar makamai daga kasashen turai zuwa HKI saboda kashe al-ummar Falasdinu.
Wani mai magana da sunan kungiyar ma’aikatan tashoshin jiragen ruwa na Italia ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Turai sun cika tashoshin jiragen ruwa na kasar da makamai wadanda ake son wadan nan lebiroro su loda su cikin jiragen ruwa don kaisu HKI.
Lebirorin sun kara da cewa basa son a dulmuyasu cikin kissan kiyashin da gwamnatocinsu suke yi a kasar Falasdinu da aka mamaye.
Labarin ya kara da cewa ma’aikan tashar jiragen ruwa a kasashen girka, Morocco da Turkiyya a fiye da tashoshin jiragen ruwa 20 sun gudanar da irin wannan zanga-zangar.