Trump Ya Ki Neman Afuwar Barrack Obama Da Maidakinsa Da Ya Kwatantasu Da Birai A Shafinsa Na “Social Trust”

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya  watsa  wani gajeren fim na gwaigwai da ya sanya kawunan mutanen da yake adawar siyasa da su a jikin

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya  watsa  wani gajeren fim na gwaigwai da ya sanya kawunan mutanen da yake adawar siyasa da su a jikin dabbobi mabanbanta, shi kuwa ya kwatanta kansa da zaki. Daga cikin wadanda aka sanya jikinsu a jikin dabbobi da akwai Barrack Obama da mai daikinsa a jikin birrrai, sai kuma Mamadani  magajin garin birnin New York da aka sanya kanshi a jikin kura.

Shi kuwa Donald Trump da aka sanya kansa a jikin zaki, ya ratsa ta tsakanin dukkanin dabbobin da su ka yi layi, tare da rusuna masa yana wucewa.

Da aka tambaye shi ko zai nemi afuwa akan wannan dan garejen fim din ya ce; Bai aikata laifi ba,amma ya yarda da akwai nuna wariya a ciki.

A jiya Juma’a ne dai aka wallafa gajeren fim din a Shafin ” Social Trust” wanda Donald Trump yake aikewa da sakwanninsa, sai dai an cire shi daga baya.Fiye da mutane 1000 ne su ka nuna fim din ya burge su a cikin kankanen lokaci sai dai kuma ‘yan siyasar kasar ta Amurka sun yi suka akai, yayin da masu goyon bayan Donald Trump suke nuna goyon bayansu.

Mai Magana da yawun fadar “White House”   Karoline Leavitt ta ce; An yi dan karamin fim din a matsayin kwaikwayon fim din “Lion King” dake nuna Donald Trump a matsayin zaki sarkin daji, bisa barkwanci.

Fadar ta White House ta bayyana fushin da mutane su ka nuna akan wannan fim ba shi da dalili, to amma daga baya kuma ta ce; an wallafa shi ne bisa kuskure.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted