Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa wawtan waziri ko shugaban gwamnatin kasar Jamus ne ya fidda kasar daga cikin tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa, a cikin watan satumban shekarar da ta gabata ce kasashen turai guda uku da ake kira Trico a takaice wato Faransa da Jamusa da kuma burtania, suka janye daga tattaunawar shirin nukliyar kasar Iran karkashin matsin lamba na wazirin kasar ta Jamus Friedrich Merz, sannan suka shigar da bukatar a sake dorawa JMI takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar Iran wadanda suka shafi shirin ta na makamashin Nukliya.
Ministan yana maida martani ne ga Merz bayan ya rubuta a shafinsa na X yana cewa yana son ya kara takurawa kasar Iran ya kuma shiga tattaunawa cikin shirinta na makamashin Nukliya don ya gaggauta kawo karshensa.
Aragchi ya ce wawtar da yayi a baya ne yasa yake nadamar matakan da suka dauka kan kasar Iran a lokacin. Banda Jamus a kwai wasu kasashen yamma da dama da suka nuna rashin iya siyasa wanda ya zama masu musiba daga baya.
Sai gashi a halin yanzu Merz yana roko a sake maida shi cikin tattaunawar don ya cimma wasu manufofinsa.