Rasha Ta Sanar Da Kawo Karshe Wa’adin Yarjejeniyar Kayyade Makaman Nukiliya Da Amurka

A jiya Laraba ne dai Rasha ta sanar da cewa daga yanzu ba za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar kayyada makaman Nukiliya da

Tashar Sararin Samaniya

A jiya Laraba ne dai Rasha ta sanar da cewa daga yanzu ba za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar kayyada makaman Nukiliya da ta kulla tsakaninta da Amurka ” Neo Start”, bayan da wa’adinta ya zo karshe a yau Alhamis.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha wacce ta fitar da wata sanarwa a jiya Larabar, ta ce; Muna kirdaron cewa  bai zama wajibi ba bangarorin da suke a karkashin yarjejeniyar Nukiliya ta ” Neo Start” su yi aiki da ita ba,amma duk da haka za mu yi aiki cikin sanin ya kamata dangane da abinda ya shafi Nukiliya.

Kasashen na Rasha da Amurka dai sun kulla yarjejeniyar kayyade yawan makaman Nukiliya ne a 2010, ta yadda yawan wuraren harba makaman da kowace kasa za ta mallaka ba zai wuce 800 ba, kuma su kansu manyan makaman Nukiliyar na kowa kar ya wuce 1,550.

Haka nan kuma bangarorin biyu sun amince da a rika gudanar da bincike domin tabbatar da abinda yake faruwa a kasa.

A gefen Amurka, har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa ba akan zuwa karshen wa’adin yarjejeniyar ta kayyade makaman Nukiliya a tsakaninta da Rasha.

Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce; A halin yanzu babu wata sanarwa da zai yi, yana mai kara da cewa; A nan gaba  Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump zai yi Magana akai.

Kasar China ta yi gargadi akan kare wa’adin yarjejeniyar tana mai cewa duniya za ta shiga cikin wani yanayi wanda ya fi na baya hatsari.                Shi kuwa Paparoma Leo na 14 ya yi kira ne da kar a koma gasar kera makamai, sannan kuma bukaci ganin an yi aiki da kyawawan halaye da bil’adama ya yi tarayya da juna akai,maimakon ci gaba da rayuwa a cikin tsoro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted