Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu nay au zai kasance dangane jawabin jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaei, kan barazanar yakin da Amurka take son dorawa JMI, wanda ni tahir Amin zan karanta.
////…Madalla, a ranar Lahadi 1 ga watan Fabarairu ne Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei, ya gabatar da jawabi a dai dai lokacinda aka fara bukukuwan cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. Sannan a cikin jawabinsa ya tabo halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, inda sojojin Amurka suka yi cincirindo da nufin farwa kasar Iran da yaki idan bata amince da bukatun Amurka ba.
Kuma wannan yana zuwa ne makonni da tashe-tashen hankulan da ita Amurka da HKI suka haddasa a kasar wanda ya lakume rayukan mutne fiye da 3000 a duk fadin kasar. Jagoran ya bayyana cewa manufar Amurka da HKI a wannan rigimar da suka tayar a cikin kasar Iran ita ce ganin bayan JMI Iran da kuma rarraba kasar don kubutar da HKI daga waragajewa, har ila yau da maida ita kasa mafi karfi a yankin gabas ta tsakiya.
Dangane da zaman dardar da ake a kasar Iran na yiyuwa shiga yaki da kasar Amurka kuma Jagoran ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata fara yaki da kowa ba, amma duk wani harin da Amurka zata kawowa kasar Iran to ta kwana da sanin cewa sai yakin sai ya game yankin gaba daya.
Masana suna ganin, idan Amurka ta kuskura ta fara yaki da kasar Iran da farko HKI tana daga cikin wadanda makaman linzamin JMI zasu nufa, sannan dukkan sansanonin sojojin Amurka wadanda suke yankin musamman wadanda suke cikin kasashen larabawa ba zasu tsira daga makaman sojojin JMI ba.
Kafin haka ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya sake tabbatar da wannan batun a hirar da ta hada shi da tashar talabijan ta CNN ta kasar Amurka a ranar Lahadi, ya kuma kara da cewa, ya na kira ga gwamnatin kasar Amurka ta yi amfani da wannan damar don cimma yarjeniya da Tehran, tare da gargadin cewa duk wani yakin da zata shiga da Iran zai yi muni kuma zai shafi dukkanin kasashen yankin.
Ya akwai yiyuwar a cimma yarjeniya tsakanin kasashen biyu a cikin dan karamin lokaci, shiga a shirin makamashin nukliya na kasar ne kawai. Ministan ya kammala da cewa, Iran ta rika ta debe kauna daga samun adalci da kuma alkawali na gaskiya daga washinton amma wasu kasashen yankin masu shiga tsakani ne kawai muke fatan suna iya yin wani abu. Don haka batun tattaunawa kai tsaye da Amurka ma bata taso ba.
A wani bangare kuma gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da Iran tare da masu shiga tsakani. Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa yan jaridu a cikin jirginda “Airforce One” kan cewa sun shiga tattaunawa da Iran, amma bai kai matsayin da zai ce an cimma matsaya ba. A lokacinda aka tambaye shi kan fasa yaki da Iran zai kara karfafata ne, Trump yace, bai ce ya fasa ba, amma zasu tattauna su kuma yi abinda ya dace, kuma har yanzun zabin kai mata hare-hare yana daga cikin zabin da yake da shi.
Masana sun bayyana cewa a lokacin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yulin da ya gabata, HKI ta gamu da makamai masu linzami na kasar Iran, wadanda tisirinsu ya bayyana a fili a biranen Tel-abib da Haifa. Har’ila yau Iran ta jefa wasu makamai masu linzami kan sansanin sojojin Amurka mafi girma a yankin gabas ta tsakiya, wato Al-udait wanda yake kasar Qatar. Kuma makaman sun yi barna mai yawa a sansanin sojokin. Mai yuwa tasirin yakin kwanaki 12 na watan Yulin shekarar da ta gaba ta, yana daga cikin abinda ya jinkirta Amurka daga kaiwa Iran hari.
Har’ila yau a hirarsa da CNN Aragchi ya ce, kada mu yi maganar abubuwanda ba za su taba yiyuwa ba, kamar maganar makamai masu linzami na kasar Iran ko kuma siyasarta a gabas ta tsakiya.
Labarin ya kara da cewa, ministan ya bayyana cewa dole ne Amurka ta daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata ta kuma amince da hakkin Iran na tashe makamashin uranium ta zaman lafiya a kuma cikin gida. Daga karshe ya bayyana cewa Iran a shirye take ta shiga yaki da Amurka idan tattaunawa tsakaninsu kasashen biyu ta kasa kaiwa ga natija.
Banda haka, yaki a wannan karon zai kasance mai tsanani ga bangarorin biyu, idan ya auku. Daga ciki babu wani sansanin sojojin Amurka a yankin wanda zai tsira daga makaman kasar Iran.
Zuwa ranar Asabr da ta gabata dai shugaba Trump bia tabbatar da cewa zai farwa kasar Iran da yaki ba,
A ranar Asabar da ta gabata dai, firai ministan kasar Qatar Sheikh Mohammad bin Abdurrahman bin Jasssim Al-Thani ya zo birnin Tehran don ganawa da jami’an gwamnatin JMI na kimani sa’o’I biyu kacal. Sannan ya koma gida. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Bakha’I ya bayyana cewa, Al-Thani ya gana da ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi da kuma sakataren majalisar koli ta kasar Iran Dr Ali Larijani.
Sannan majiyar gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa, a haduwar Al-Thani da jami’an gwamnatin kasar Iran a Tehran suna kokarin rage tsananin tashin hankalin da ake fama da shi a yankin, mai yuwa kuma har da dakatar da aukuwar yaki.
A halin yanzu dai yaki yana iya barkewa a ko wani lokaci, ganin yadda ko wani bangare y adage a kan matsayinsa.