Jagora: Idan Amurka Ta Kunna Wutar Yaki A Wannan Karon Zai Game Wannan Yankin Baki Daya

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  wanda yake Magana akan abinda yake faruwa, ya yi Ishara da Amurka yana mai cewa: “Babu

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  wanda yake Magana akan abinda yake faruwa, ya yi Ishara da Amurka yana mai cewa: “Babu wani sabon abu a cikin abinda suke yi, domin wani lokaci suna Magana akan yaki da aiko da jiragen sama da na ruwa da sauransu.”

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce; “A baya, Amurkawa sun sha yin barazana a cikin maganganunsu, suna cewa suna da dukkanin zabi akan teburi daga ciki har da yaki.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Ya kamata Amurkawa su san cewa a wannan karon idan yaki ya barke, to zai shafi dukkanin wannan yankin ne.”

Haka nan kuma ya yi Ishara da Trump yana mai cewa; “Wannan mutumin yana ta nanata cewa, mun aiko da jiragen yaki… ko kadan bai kamata al’ummar Iran su ji ko gizau ba, dama irin wannan barazanar ba ta yin  tasiri akan al’ummar Iran.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; “Ba mu ne wadanda za su fara yaki ba, ba mu da aniyar kai wa wata kasa hari,amma al’ummar Iran zai mayar da martani mai karfi akan duk wanda ya kawo masa hari, ko ya takura masa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted