Kungiyoyin Falasdinawa Sun Yi Tir da Hare Haren HKI Kan Ofishin Jakadancin Iran A Siriya

Kungiyoyin Falasdinawa sun yi tir da allawadai da hare haren jiragen yakin HKI kan karamin ofishin jakadancin JMI da ke birnin Damascus na kasar Siriya

Kungiyoyin Falasdinawa sun yi tir da allawadai da hare haren jiragen yakin HKI kan karamin ofishin jakadancin JMI da ke birnin Damascus na kasar Siriya a ranar Litinin. Sun kuma kara da cewa, wadannan hare haren sun nuna gazawar HKI na kaiwa ga manufofinta a yankin da take fafatawa da kungiyoyin Falasdinawa a zirin Gaza da kuma magoya bayansu a sauran kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar kungiyoyin falasdinawa suna cewa ayyukan ta’addanci wanda HKI ta yi a Gaza da Lebanon da siriya sun nuna cewa samuwar HKI ya girgiza, kuma akwai yiyuwan ta rushe, kuma kawancen masu gwagwarmaya a yankin suna samun nasara a kanta da kawayenta.

Daga karshe kungiyoyin sun bayyana cewa hare haren na Damascus hare hare kan dukkan kasashen Larabawa da kuma kasashen musulmi. Kuma yakamata a ladabatar da ita da wasu karin hare hare masu karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments