Amurka Tana Amfani Da Yakin Kwakwalwa Domin Kawo Tarnaki Ga Batun Tsaron Yankin

shugaban kasar iran Masud Pezeshkiyan yayi gargadin cewa motsin dakarun sojin Amurka a yankin yammacin Asiya wani bangaren ne na kokarin da Amurka keyi na

shugaban kasar iran Masud Pezeshkiyan yayi gargadin cewa motsin dakarun sojin Amurka a yankin yammacin Asiya wani bangaren ne na kokarin da Amurka keyi na yamutsa batun tsaro a yankin yammancin Asiya

shugaban yayi wannan tsoka ci ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da yarima mai jiran gado na kasar Saudiya mohammad bin salman a jiya talata, bayan isar jirgin yakin Amurka yankin da kuma barazanar da amurka ke ci gaba da yi,bayan da wasu jami’anta suke zargin iran da yin amfani da karfi wajen murkushe masu tada tarzoma.

yace mun cimma matsaya da kasashen turai a tattaunawar da aka yi , amma amurka ta lalatashi, a wajensu tattaunawa itace a aiwatar da abin da suke so, wanda wannan ba shi ne tattaunawa ba.

daga karshe pezeshkiyan ya jinjinawa kasashen musulmi game da goyon bayan da suka bawa iran musamman kasar saudiya a lokacin yaki kwanaki 12, yace hadin kai tsakanin kasashen musulmi itace sahihiyar hanyar samar da tabbataccen zama lafiya a yankin, yace gwamnatocin kasashen musulmi suna da rawa mai muhimmanci da za su taka a wannan bangaren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted