IRGC Ta  Sake Fitar Da Bayani  Akan Ayyukan Ta’addancim Da Su Ka Faru A Iran

Bangaren leken asiri na dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran “IRGC” ya fitar da sanarwa wacce ta kunshi cewa a yayin hare-haren da

Bangaren leken asiri na dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran “IRGC” ya fitar da sanarwa wacce ta kunshi cewa a yayin hare-haren da ‘yan ta’adda su ka rika kai wa a cikin biranen Iran, mutanen gari sun  kira su ta wayoyo har sau 400,000 suna bayar da bayanai akan masu aikata ta’addanci da hakan ya taimaka matukuma.

Bayanan sun kunshi ‘yan ta’adda da mabarnata da su ka taka rawa wajen kama da dama daga cikinsu.

Haka nan kuma bayanin ya ci gaba da cewa; A bisa wadannan bayanan da mutane su ka gabatar, an rusa kungiyoyin ‘yan ta’adda an kuma gano wasu tun kafin su kai ga aitawar da barna.

Haka nan kuma an kama wasu mutane 31 wadanda suke da alaka kai tsaye da ‘yan sahayoniya suna bayyana shirinsu na yin aiki da Mosad.

Dakarun na IRGC sun kuma bayyana cewa, tare da cewa an dakile mafi girma na Shirin makiyan,amma ana ci gaba da sa ido ta fuskar tattara bayanan sirri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted