Hamas Ta yi Maraba Da Sanarwar Da Amurka Ta Fitar Na Fara Aiki Da Mataki Na 2 Na Yarjejeniya

Babban jami’I a kungiyar gwagwarmaya ta Hamas yayi lale marhabin da sanarwar da kasar Amurka ta fitar na fara aiki da mataki na 2 na

Babban jami’I a kungiyar gwagwarmaya ta Hamas yayi lale marhabin da sanarwar da kasar Amurka ta fitar na fara aiki da mataki na 2 na yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da Isra’ila da zai kawo karshen kisan kare dangin da ta ke yi a Gaza.

Taher Nunu shi ne yayi wannan bayani kwana daya bayan da manzon musamman na Amurka a yankin yammacin asiya steve witkoff ya bayyana a shafinsa na X cewa za’a aiwatar da mataki na 2 na shirin da Shugaban Amurka Donald trump ya bullo da shi kan rikicin gaza, yace zai ci gaba daga yarjejeniyar farko da aka amince da ita zuwa karshen shekarar da ta gabata na kawar da makamai da harkokin fasa da kuma sake gina yankin

Nunu mai bada shawara ga shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas yayi maraba da kafa kwamitin kwararru da aka yi, kana ya bayyana bukatar bude mashigar rafah domin bada dama a shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza da kuma janyewar sojojin mamayar Isra’ila daga yankin na gaza.

Israila na kokarin kaucewa cika alkawuran da ta dauka a harjejeniyar dakatar da bude wuta, sai dai masu shiga tsakanin suna kokarin matsin lamba kan gwamnatin tayi aiki da nauyin dake kanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted