A hukumance kasar Amurka ta ayyana bangaren kungiyar muslim brotherhood a kasashen masar, labanon da kuma Jodan a matsayin yan ta’adda wanda hakan ke nuna karuwar yakin da Washington ke yi da kungiyoyiin da take ganin barazana ne ga muradun isra’ila a yankin yammacin Asiya.
An sanar da wannan matakin ne a jiya talata bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta musamman da ta umarci gwamnatinsa fara aiwatar da sanya sonayen kungiyoyi cikin jerin sunayen da ba’a amince da su ba.
Ana shi bangaren salah Abdel haq shugaban rikon kwarya na kungiyar ikhwanul musulmin na kasar Masar yayi watsi da wannan mataki na trump, kuma yace kungiyar za ta kalubalanci wannan mataki ta hanyoyin shari’a. kuma za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta domin karya wannan mataki da zai cutar da miliyoyin ‘yayan kungiyar a fadin duniya
A bangren guda kuma ministan harkokin wajen kasar Masar yayi maraba da matakin na Trump na ayyana kungiyar ikhwanul muslmin ta kasar masar a matsayin yar ta’adda, kuma ya bayyana shi a matsayin mataki na jarumta, kuma ya nuna irin yadda ake kiran kungiyar da bala’I ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.