Rahotananni da suka fito daga yankin Gaza sun bayyana cewa daga lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas da Amurka ta bullo da shi a watan oktoban da ya gabata HKI ta rusa gidajen falasdinawa guda 250 .
Israila tana share dukkan yankunan daga taswira, kamar yadda mohammad Al astal wani mai fashin baki a yankin Gaza ya bayyana, yace sojojin ISra’ila suna rusa duk wani da suka gani a gabansu, gidaje makarantu, kamfanoni, da layuka kuma babu wata hujja ta tsaro dake tabbatar da abin da suke aikatawa.
Isra’ila ta kashe falasdinawa sama da 71000 daga lokacin da ta kaddamar da yakin kare dangi a yankin gaza daga 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 bayan ambaliyar aqsa da falasdinawa suka yi a matsayin mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai musu ba dare ba rana.
An kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta ne a watan oktoban da ya gabata, sai dai gwamnatin tel aviv tana ci gaba da keta yarjejeniyar da yin kunne uwar shego da kiraye- kirayen da ake mata na tayi aiki da yarjejeniyar.